
Mai magana da yawun hukumar Ikechukwu Ani ya bayyana haka a wata sanarwar da ya rabawa manema labarai yau sakamakon takkadamar da ta biyo bayan kin ritayar Sufeto Janar Kayode Egbetokun wanda ya cika shekaru 60 tun bara. Ani ya ce hukumar ba za ta amince da duk wata dokar da ta sabawa ta aikin gwamnati mai lamba 020908 sakin layi na 1 da na 2 ba.
Kakakin hukumar yace sun sauya matsayin su dangane da cece kucen da ya biyo karin lokacin da aka yiwa Egbetokun abinda ya haifar da guna guni daga manyan jami'an 'yan sandan wadanda suke fatar maye gurbinsa.
Ani yace bayan wani taro da hukumar kula da aikin 'yan sandan ta gudanar a ranakun 27 da 28 na wannan wata, ta bukaci duk wani 'dan sandan da ya cika shekara 60 a duniya ko kuma ya cika shekaru 35 a bakin aiki da ya gaggauta tube kakinsa domin tafiya ritaya.
Ani ya ce tuni aka aikewa da Sufeto Janar Egbetokun umarnin hukumar domin aiwatar da ita nan take bayan taron da mataimakin Sufeto Janar mai ritaya Hashimu Argungu ya jagoranta.
Wannan sanarwa na iya haifar da rudani da kuma takun saka tsakanin hukumar da kuma ofishin Sufeto Janar.
An dade ana korafi dangane da tsawaita lokacin aikin Sufeto Janar Egbetokun musamman daga manyan jami'an 'yan sandan, sai dai wasu na cewa wannan ba shi ne karo na farko da ake karawa mai rike da kujerar lokaci ba.
Tsohon kwamishinan 'yan sanda Muhammad Indabawa ya ce hukumar kula da aikin 'yan sanda bata da hurumin nadi da kuma ladabtar da Sufeto Janar, sai dai shugaban kasa da majalisar kasa da ta kunshi shugaban kasa da gwamnonin jihohi da kuma ministan Abuja tare da tsoffin shugabannin kasa da manyan alkalai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI