Hukumar kare hakkin ɗan'adam din ta ce wani bincike da aka gudanar ba a gano wata shaida da ke nuna cewa sojojin Najeriya sun ci zarafin mata da kananan yara da gangan, ko kuma gudanar da ayyukan zubar da ciki a asirce ba, a yakin da suke fafatawa da ‘yan ta’adda a yankin arewa maso gabashin ƙasar.
Hukumar haƙƙin bil’adama da gwamnatin Najeriiya ta baiwa aikin binciken, ta dauki tana binciken wasu rahotanni uku na kamfanin dillancin labaru na Reuters da aka buga a watan Disambar 2022, wadanda suka gano cewa sojojin Najeriya sun gudanar da wani shiri na sirri, da aka zubar da cikin wasu mata ba bisa ka'ida ba, tare da kashe yara kanana a yankin arewa maso gabashin ƙasar, da aka shafe sama da shekaru 15 ana fama da ayyukan ta’addanci.
Hukumar ta ce babu wata shaida da aka samu data tabbatar da anyi wannan ɗanyen aikin
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI