Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar a Najeriya Abdullahi Maiwada a wata sanarwa da ya fitar ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan samun amincewar haka daga ofishin mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan sha’anin tsaro.
Majalisar wakilan Najeriya a ranar 11 ga watan disamba ta ɗorawa kwamitinta mai lura da hukumar kwastam ya binciki ayyukan da hukumar ke yi a iyakokin ƙasar bayan zarginsu da aka yi da taimakawa ƴan sumoga da kuma cin zarafin ƴan Najeriya.
Wannan ya biyo bayan wani ƙudirin gaggawa da ɗan majalisa Sesi Whingan ya gabatar, inda ya ce maimakon daƙile simoga jami’an kwastam a iyakokin ƙasar na bigewa da taimakawa masu fasa ƙwauri.
To sai dai mai magana da yawun hukumar hana fasa ƙwaurin ta Najeriya a sanarwar da ya fitar ya ce matakin rushe tawagar na a matsayin wani yunƙurin ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro wurin ƙarfafa tsaro a iyakokin ƙasar.
Maiwada ya ce rushe wannan tawaga ba zai kawo tsaiko ba ko kaɗan dangane da tsaron iyakokin Najeriya ko kuma kasuwanci, illa hakan wani mataki ne da zai zamanantar da ayyyukan hukumar ta Custom da ayyukanta da kuma tabbatar da tsaron Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI