Mai magana da yawun hukumar Funmi Oguntala, ta shaida wa jaridar Premium Times da ake bugawa a ƙasar cewa, sun dakatar da kama motoci ko kuma cin tara saboda sun ɗaukaka ƙara a game da hukuncin da kotu ta yanke, to amma da zarar suka samu nasara a shara’ar, to ko shakka babu za su ci gaba da ayyukansu kamar yadda suka saba.
Kotu ta haramtawa VIO daga kamawa ko kuma cin tarar masu ababen hawa a Najeriya. © Daily TrustA ranar 5 ga watan nuwamba mai zuwa ne ake dakon cewa kotun ɗaukaka ƙara ta tarayya da ke Abuja za ta yanke hukunci a game da ƙarar da hukumar VIO ta shigar dangane da wannan batu.
Harabar babbar kotu Tarraya AFP - KOLA SULAIMONTo sai dai yayin da hukumar reshen birnin Abuja ke cewa cewa tana mutunta umarnin kotu, reshen hukumar a jihar Legas ya ce wannan mataki bai shafe ta, domin kuma a Legas akwai dokoki na musamman da ke daidaita zirga-zirgar ababan hawa a kan tituna, kuma watakila Abuja da sauran jihohi ba su da irin waɗannan dokoki ne saboda haka kotun ta ba su wancan umurnin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI