Harin sojin saman Najeriya ya sake hallaka tarin fararen hula a Zamfara

Harin sojin saman Najeriya ya sake hallaka tarin fararen hula a Zamfara

Rahotanni sun bayyana cewa tun farko ƴan sa kan da ke taimakawa wajen fatattakar ƴan bindiga a ƙauyukan ne suka nemi ɗauki don taimakawa musu wajen kammala murƙushe ƴan bindigar da suke tsaka da faɗa da su, amma kuma Sojojin saman na Najeriya suka yi tsammanin su ne ƴan bindigar inda nan ta ke suka buɗe musu wuta.

Tuni dai gwamnan jihar ta Zamfara Dauda Lawal ya aike da saƙon jaje ga iyalai da ƴan uwan ƴan sa kan da suka mutu a wannan hari yayinda ya jinjinawa Sojin na Najeriya game da namijin ƙoƙarin da suke wajen kakkaɓe barazanar ƴan bindiga a jihar.

Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta miƙa sakon ta’aziyya kan kisan ƴan sa kan waɗanda ta ce sun nuna matuƙar jajircewa a wanzar da zaman lafiya ga al’ummar ta Tungar Kara a ƙaramar hukumar Zurmi wajen kange barazanar ƴan bindigar da ke afkawa jama'a.

Rahotanni sun ce ƴan sa kan, na kan hanyarsu ta barin Gidan Makera ne na yankin Boko duk dai a ƙaramar hukumar ta Zurmi lokacin da haɗarin ya faru a yau Lahadi, da ya kai ga rasa rayukan 16 daga cikinsu.

Wannan tsautsauyi na zuwa a dai dai lokacin da wasu ƴan sa kan fiye da 30 suka rasa ransu cikin makon jiya can a jihar Katsina bayan da wani gungun ƴan bindiga ya afka musu, lamarin da ke nuna gagarumar asarar da aka fuskanta a ƙoƙarin da fararen hula ke yi na bai wa kansu kariya daga barazanar ƴan bindiga.

A cewar wasu bayanai tsautsayin ya faru ne a lokacin da Sojin saman na Najeriya ke kan hanyarsu ta dawowa daga luguden wutar da suka yi wa maɓoyar ƴan bindigar a garin na Tungar Kara yau lahadi, kwatsam kuma sai suka ci karo da ayarin ƴan sa kan dalilin ya sanya suka tsammaci cewa ƴan sa kan, wani ɓangare ne na ƴan bindigar suke ƙoƙarin guduwa.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Sojin Najeriya ke kashe tarin fararen hula ko kuma ƴan sa kai ko ma ƴan gudun hijira bisa tsammanin kasancewarsu ƴan bindiga ko ƴan ta’adda ba.

Masana dai na alaƙanta kuskuren kisan ƴan sa kan, da yadda ake gaza musayar bayanai tsakanin irin waɗannan mutane da ke taimakawa zaman lafiyar yankuna da kuma jami’an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)