
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Jaridar Dailiy Trust da ake wallafa wa a ƙasar cewar, lamarin ya faru ne a lokacin da ake gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin a ranar Asabar da ta gabata, inda ƴanbindigar suka yi ƙoƙarin kai hari cikin garin.
To sai dai ƙoƙarin dakatar da harin da jami’an tsaron sun yi ne dai ya haifar da musayar wuta tsakaninsu da ƴanbindigar, wanda ya yi sanadiyar ƴansanda 2 da ɗanbanga guda.
Bayan faruwar lamarin ne jirgin yaƙin sojoji ya kai harin, kuma da alama ya zo ne don taimaka wa jami’an tsaro, inda ya jefa bom a Unguwar Yauni da ke kudancin Zakka, kuma mutane 6 ƴan gida ne suka mutu sannan wata mata ta samu raunuka.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da jirgin yaƙin sojojin Najeriya, ya taɓa kai harin kuskure a jihar Katsina ba da ya yi sanadiyar mutuwar mutane.
Ko a watan Yulin shekarar 2022, sai da wani harin kuskuren jirgin sojin Najeriya ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2 a ƙauyen Kunkunni da ke ƙaramar hukumar ta Safana.
Kawo yanzu dai rundunar sojoji da kuma ta ƴansanda basu ce komai dangane da harin na ranar Asabar ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI