Ya dai bayyana hakan ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai, bayan isowarsu filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, da safiyar Laraban nan.
A lokacin zantawarsa da jaridar OwnGoalNigeria a birnin Kigali na kasar Rwanda, Eguavoen ya shaidawa jaridar cewar ya kammala aikin da aka bashi na jagorantar tawagar, a wasanni biyu da tayi na sharar fagen zuwa gasar lashe kofin Afrika tsakaninta da Jamhuriyar Benin da kuma Rwanda.
To sai dai a yanzu Eguavoen ya ce zai tattauna da shugabannin Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya NFF, don sanin yadda makomarsa game da ragowar wasannin sharen fagen da suka yi saura don sanin yadda za su kasance.
A wasanni biyu da mai horaswan ya jagoranci Super Eagles, ya samu nasara a wasan da ya yi da Jamhuriyar Benin da ci 3 da nema, sai kuma canjaras da ya yi da Rwanda.
Hukumar NFF ta naɗa Eguavoen ne kwanaki kadan gabanin wasaninta na sharen fagen, bayan da ta raba gari da sabon mai horaswa ɗan ƙasar Jamus Bruno Labbadia, sakamakon rashin cimma matsaya dangane da batun haraji.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI