Har yanzu Najeriya ba ta kama hanyar yaƙi da rashawa ba - Bankin Duniya

Har yanzu Najeriya ba ta kama hanyar yaƙi da rashawa ba - Bankin Duniya

Bankin duniyar da sauran masu ruwa da tsaki sun buƙaci gwamnati da ta yaƙi ayyukan cin hanci da rashawar domin ita kaɗai ce hanya ɗaya tilo ta bunƙasar tattalin arziƙi.

A wani taron tattaunawa kan halin da aikin yaƙar cin hanci da rashawa ke ciki a Najeriya wanda ƙungiyar Agora Policy haɗin gwiwa da gidauniyar MacArthur suka shirya a jiya Talata, mahalarta taron sun nemi a sauya fasalin tsarin siyasar Najeriya da na shari’a tare da gina manyan hukumomin yaƙi da rashawa.

Wakilin Bankin Duniya a Najeriya, Ndiame Diop ya ce cin hanci ya zama babban ƙalubale ga fannin tattalin arziƙin ƙasar, inda ya ƙara da cewa samar da tsaftataccen tsari a aikin gwamnatin ƙasar ya zama babban al’amari da aka kasa cimmawa.

Daraktan Gidauniyar MacArthur a Afrika, Kole Shettima ya bayyana cewa cin hanci da rashawa babban naƙasu ne ga ci gaban Najeriya ta kowani fanni.

Wannan dai na zuwa dai-dai lokacin da gwamnatin Najeriya ke cewa ta na samu ci gaba a ayyukan yaƙi da cin hanci da rashawar, inda ko a baya-bayan nan hukumar EFCC mai yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin ƙasar ta’annati ta ce ta karɓe wani rukuni mai ƙunshe da gidaje 753 mallakin wani tsohon babban jami'in gwamnati, nasara mafi girma da ta taɓa samu a cikin sama da shekaru 21 da kafuwarta.

Bayan fitar wannan batu ne kuma al’ummar ƙasar da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum suka fara faɗar mabanbantan ra’ayoyi, musamman kan rashin bayyana sunan jami’in gwamnati da ya aikata wannan badaƙala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)