Har yanzu hajarin VAT na nan a kashi 7.5 - Ministan kudin Najeriya

Har yanzu hajarin VAT na nan a kashi 7.5 - Ministan kudin Najeriya

Ministan ƙudin ƙasar wanda kuma ke jagorantar kwamitin kula da tattalin arzikin Wale Edun ne ya ƙaryata zargin, a wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kansa a litinin din nan.

Edun ya tabbatar da cewar babu ƙarin da aka samu a harajin na VAT, domin abu ne da ya ce ya ginu bisa ginshikai uku na dokokin harajin ƙasar.

Har yanzu harajin VAT na nan akan kashi 7.5 kuma wannan ne abinda gwamnati ke karba kan duk wata haja da ke da haraji. Don haka babu wata hukumar gwamnati ko cibiya da zata amshi sama da hakan.

Ya yinda da yake nuna damuwarsa game da tsauraran matakan da gwamnatin ƙasar ke ɗauka a bangaren tattalin arziƙi, Edun ya baiwa ƴan Najeriya haƙuri tare da tabbacin cewar an samar da su ne don kawar da fatara da kuma ci gaban tattalin arziƙin ƙasar.

Idan dai ba a manta ba, a makon daya gabata ne aka fara yada rahotannin da ke cewar gwamnatin Najeriya ta ƙara ƙudin harajin VAT, daga kashi 7 da biyar zuwa kaso 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)