Har yanzu Faransa na da matukar tasiri a Afirka - Masana

Har yanzu Faransa na da matukar tasiri a Afirka - Masana

Alain Antil, mai bincike a kan harkokin siyasar yankin Sahel a Cibiyar kasashen duniya dake Paris ta FRI yace wannan matsayi ya fi tasiri a kasashen dake amfani da Turancin Ingilishi wadda kasar ba ta yiwa mulkin mallaka ba.

Ganin yadda mazauna karkara ke tururuwa zuwa birane a Afirka da kuma yadda ake hasashen samun karuwar sama da dubu 700 nan da shekarar 2050, wanda zai samar da mutanen da ba attajirai ba kuma ba talakawa ba, kasashen dake nahiyar Afirka na fatar cin gajiyar zuba jarin da Faransa ke yi domin bunkasa tattalin arzikin su.

Alkaluma sun nuna cewar Najeriya ce kasa ta farko da ta fi gudanar da harkokin kasuwanci da Faransa a shekarar 2023, sannan Afirka ta Kudu dake bi mata baya.

Saboda haka shugaban Faransa Emmanuel Macron ke daukar matakan ganin wadannan harkokin kasuwanci sun dore a tsakanin kasashen biyu, da zummar ganin kowanne bangare ya amfana.

Kungiyar ‘yan kasuwar Faransa da Najeriya da Macron ya kafa a shekarar 2018 lokacin da ya kai ziyarar aiki a Najeriya, na taka rawa wajen karfafawa masu zuba jari da harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.

Ana saran mambobin wannan kungiyar a karkashin jagoranci Abdusamad Rabiu su gana da Macron yayin wannan ziyarar, kuma cikin su akwai Alhaji Aliko Dangote, mutumin da ya fi kowa arziki a Afirka, tare da fatar kulla sabbin yarjeniyoyin kasuwanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)