Yayin da wasu bayanai ke cewa akwai sojoji da dama da har yanzu ba a gano inda suke ba, bayan kazamin gurmurzun da aka yi, rundunar sojin Najeriya ta nanata cewa a iya saninta, dakarunta 6 ta rasa yayin da ta samu nasarar kashe ‘yan ta’adda 34.
Mayaƙan ISWAP akan motoci da babura ne suka ƙaddamar da hare-hare a ranar Lahadi a sansanin soji da ke Sabon Gari a Damboa ta jihar Borno.
Mayaƙan sun bankawa sansanin wuta tare da kone ababen hawan soji kamar yadda majiyar sojin da bata yadda a ambaci sunanta ba ta tabbatar.
Sojojin 6 sun rasa rayukansu bayan artabu da ƴan ta’addan da suka kai musu hari, abin da ya tirsasawa sojin janyewa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI