Har yanzu a na ci gaba da baiwa jihar Borno gudunmuwa bayan ambaliyar ruwa

Har yanzu a na ci gaba da baiwa jihar Borno gudunmuwa bayan ambaliyar ruwa

A cikin sanarwar da mai taimakawa gwamnan jihar wajen hulda da kafofin yada labarai Abdurrahman Ahmed Bundi ya fitar, ta ce an samar da gudunmuwar ce don tallafawa waɗanda abin ya shafa.

Sanarwar ta ce izuwa yammacin jiya Laraba, gwamnatocin jihohin da suka bada agaji kawo yanzu sune jihohin Bauchi da Kebbi da suka bada naira miliyan dari biyu biyu, sai jihohin Yobe da Kano da Gombe da Taraba da kuma Katsina da suka bada naira miliyan dari dari, yayin da jihar Adamawa ta bada naira miliyan 50.

Yadda ake gudanar da aikin agaji a Maiduguri Yadda ake gudanar da aikin agaji a Maiduguri AFP - AUDU MARTE

Daga cikin waɗanda suka bada agajin akwai Alhaji Aliko Dangote da ya bada naira biliayan biyu da Alhaji Aminu Dantata naira biliyan daya da rabi, Alhaji Atiku Abubakar naira miliyan dari, ɗan takarar jam’iyar Labour a zaɓen daya gabata Peter Obi naira miliyan 50, tsohon shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan naira miliyan 50, uwar gidan shugaba Tinubu miliyan dari 5.

Jerin sunayen waɗanda suka bada ƙudi

1. Alhaji Aliko Dangote, Biliyan 2

2. Alhaji Aminu Dantata, Biliyan daya da rabi

3. Alhaji Atiku Abubakar, Miliyan dari

4. Peter Obi, Miliyan 50

5. Hukumar Ci gaban shiyar Arewa Maso Gabas, Biliyan 3

6. Majalisar dattawa, Miliyan 54 da dubu dari 5

7. Majalisar wakilai, Miliyan dari

8. Jami'iyar PDP, Miliyan 25

9.Majalisar dokokin jihar Borno, Miliyan 60

10. Tsohon shugaban majalisar Dattawa Ahmed Lawan, Miliyan 50

11. Hon Zainab Gimba, Miliyan 25

12. Ibrahim Abba Umar, Miliyan 50

13. Sumaila Satumari, Miliyan 20

14. Hon Mallam Gana Kareto, Miliyan 10

15. Ƙungiyar sanatocin Arewacin Najeriya. Miliyan 10

16. Sen Barau Jibril, Miliyan 10

17. Hon Moh’d Abubakar Maifata, Miliyan 50

18. Yankin Kudancin Borno, Miliyan dari 2

19. Hon Zakariya Dikwa, Miliyan 10

20. Al-Amanah Aid, Miliyan 1

21. Hon Mohammed Imam Miliyan 50

22. Maina Ma’aji Lawan, Miliyan 10

23. Alhaji Ali Modu Sheriff, Miliyan dari

24. Hon Dr Ali Bukar Dalori, Miliyan 10

25. Sen M.T Monguno, Miliyan 50

26. Sen Kaka Shehu, Lawan Miliyan 50

27. Hon Aliyu Betara, Miliyan 100

28. Hon Abdulkadir Rahis, Miliyan 25

29. Hon Ibrahim Abuna, Miliyan 25

30. Hon Usman Zannah, Miliyan 10

31. Hon Engr Bukar Talb, Miliyan 10

32. Hon Yerima Lawan Kareto, Miliyan 2

33. Abdussalam Kachallah, Miliyan 100

34. Awari Usman Alkali, Miliyan 20

35. Kamfanin EEC, Miliyan 50

36. Kamfanin gine-gine na Dan Nene, Miliyan 30

37. Uwar gidan shugaban kasa Oluremi Tinubu, Miliyan dari biyar

38. Dauda Kahutu (Rarara), Miliyan 10

39. Kananan hukumomin Borno 27, Biliyan daya da miliyan 350

40. Kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya, Miliyan 10

Har wayau, bayaga gudunmuwar ƙuɗi, akwai kuma waɗanda suka bada gudunmuwar kayayyaki.

Jerin sunayen waɗanda suka bada kayayyaki

1. Hukumar ci gaban yankin Arewa maso Gabas ta bada buhunnan shinfa masu nauyin kilo 25 guda dubu 20 da katan dubu 20 na makaroni da kuma jarakunan man gyara dubu 10.

2. Kamfanin sanar da kayan abinci na Sumal Food Group da ke Ibadan na jihar Oyo, ya bada burodi dubu 50 da biskit katan dubu 5.

3. Gwamnatin jihar Nasarawa ta bada tirela 2 na shinkafa biyu na taliya sai kuma biyu na suga.

4. Janar Buba Marwa mai ritaya ya bada tirela 10 na takin zamani. 

5. Hon Aminu Jaji buhu dari 6 na shinkafa.

6. Ƙungiyar Injiniyo ta Najeriya reshen jihar Borno ta bada atamfa dubu 10.

7. Engineer Usman Monguno atamfa dubu 10.

8. Alhaji Abdulkadir Ali kayayyaki na kusan naira miliyan dari da 20.

9.Ƙungiyar injiniyoyi ta Najeriya ta bada gudunmuwar kayan gwanjo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)