Gwamnonin Najeriya sun amince da ƙudirin gyaran dokar haraji

Gwamnonin Najeriya sun amince da ƙudirin gyaran dokar haraji

Takaddar mai ɗauke da sa hannun shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq ayyana sabon tsarin da za’a raba harajin tsakanin jihohi.

Ƙungiyar ta ce za'a raba kashi 50 na harajin da ake tarawa a ƙasar daidai tsakanin kowaccce jiha. Za kuma a raba kashi 30 bisa gudunmawar da kowaccce jiha ta bada wurin tara haraji. Sai kuma kashi 20 za a raba daidai da yawan alumma a kowaccce jiha.

Sai dai kungiyar ba ta amince da karawa al’umma ƙasar haraji ba, wanda shima yake kunshe cikin sabuwar dokar.

Kungiyar ta kuma buƙaci a cire wasu kayyakin buƙata da kuma kayan noma daga cikin jerin kayayyakin da za a biyawa harajin VAT a ƙasar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)