Har wayau, a cikin matsayar da ƙungiyar ta cimma bayan taron, akwai ƙin amincewa da sabon ƙarin harajin kayayyaki na VAT gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar dokoki ta ƙasar don amincewa da shi.
A ranar 3 ga watan Oktoban da muke ciki ne dai shugaba Tinubu ya aike wa majalisar wakilan ƙasar ƙudurin, a lokacin da ya ke hutu a birnin London, wanda shugaban majalisar Abbas Tajuddeen ya karanto.
Tinubu ya ce an tsara sabbin kudirin dokar harajin ne don tallafa wa manufofin gwamnatinsa, da kuma ƙarfafa cibiyoyin hada-hadar kudin ƙasar.
Da yake bayyana matsayarsu kan lamarin, shugaban ƙungiyar kuma gwamnan jihar Gombe Yahaya Inuwa, ya ce ɗaukar wancan mataki da gwamnati ke shirinyi al'ummarsu ne zai shafa.
Taron dai ya samu halartar gwamnan Kaduna Uba Sani da Inuwa Yahaya na Gombe da Dauda Lawal Dare na Zamfara da Abdullahi A. Sule na Nasarawa da Babagana Zulum na Borno da Bala Mohammed na Bauchi da AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara da Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa sai kuma sauran gwamnonin yankin da suka samu wakilcin mataimakansu.
Hakan taron ya samu halartar Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, da sarakunan da suka haɗa da mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III da shehun Borno Alhaji Abubakar Ibn Umar Garba Al- Amin El-Kanemi da sarkin Zazzau Malam Ahmad Nuhu Bamalli da Ohinoyi na ƙasar Ebira Alhaji Ahmed Tijani Anaje da Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar da sarkin Kazaure Alhaji Najib Hussaini Adamu da Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu da Sauransu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron rahoton wakilinmu na Kaduna Aminu Sani Sado.......
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI