Gwamnatin Tinubu ba za ta sauya matakanta ba - APC

Gwamnatin Tinubu ba za ta sauya matakanta ba - APC

Jam'iyyar ta kuma yi watsi da iƙirarin ƴan adawa na tafka maguɗi a zaɓen gwamnan jihar Edo da ya gudana a ranar 21 ga watan Satumban da ya gabata.

A ranar Alhamis ɗin nan ne, Kwamitin Amintattu na Jam'iyyar adawa ta PDP ta yi zargin cewa, APC ta tafka maguɗi a zaɓen Edo domin cimma wata manufa ta mayar da Najeriya kan tsarin jam'iyya guda da ke mulkin har abada a kasar.

A yayin gabatar da jawabi ga manema labarai a birnin Abuja, shugaban jam'iyyar PDP, Sanata Adophus Wabara ya bayyana damuwarsa kan halin da Najeriya ke ciki na taɓarɓarewar tattalin arziki, matsalar da ya ce, tsare-tsaren gwamnatin APC ne suka haddasa.

Sai dai a yayin mayar da martani a yau Juma'a, Darektan Yaɗa Labarai na APC, Alhaji Bala Ibrahim, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa, ko koɗan jam'iyyar ta APC ba ta aniyar wargaza dimokurɗiyyar Najeriya.

Ibrahim said, “The APC as a ruling party is not intending to foist on the country anything that is going to injure democracy.

Da dama daga cikin ƴan Najeriya na ci gaba da kokawa kan matakan gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da suka ce sun jefa su cikin ƙuncin rayuwa, inda a baya-bayan aka ƙara samun tashin farashin litar man fetur a daidai lokacin da takawa ke kokowa kan tsadar rayuwa.

Kodayake gwamnatin Tinubu ta ce, babu hannunta a ƙarin farashin na baya-bayan nan.

Amma ƴan Najeriya na ƙorafin cewa, ai shugaba Tinubu da kansa ya sanar da janye tallafin man fetur tun a ranar da aka rantsar da shi a matsayin magajin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)