Gwamnatin Najeriya za ta raba tan 1,500 na Irin alkama

Gwamnatin Najeriya za ta raba tan 1,500 na Irin alkama

Shugaban shirin a matakin ƙasa, Ibrahim Mohamed Arabi ne ya bayyana haka, a ziyarar da ya kai wani kamfanin takin zamani a ƙaramar hukumar Madobin jihar Kano.

Arabi ya ce sabon Irin zai taimaka wajen magance ƙarancin alkama da tsadarta, yayin da a gefe guda zai tallafawa ƙananan manoma. Ya ƙara da cewa kamfanin Al-Yuma da ke samar da Iri, taki, da sauran kayayyakin noma na Jihar Kanon ne zai samar da Irin alkamar.

A zantawarsa da RFI Hausa, shugaban ƙungiyar manoman Najeriya AFAN, Dr Farouk Rabi'u Mudi, ya ce matakin zai yi tasiri matuƙa wajen kawo cigaban fannin noma musamman na alkama.

Dr Farouk ya kuma ce cigaban zai inganta yanayin yadda ake samar da alkama, kasancewar ita bata fitowa a lokacin zafi, sai dai samar da wannan Iri mai jure zafi zai sanya a samu wadatarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)