Gwamnatin Najeriya za ta farfado da masakun da ke sassan kasar

Gwamnatin Najeriya za ta farfado da masakun da ke sassan kasar

Tawagar bada shawara kan auduga da ake kira ICAC ta samu jagorancin Babban Daraktanta, Eric Trachtenberg.

Ma’aikata da masana a fanin da ya shafi auduga a bangaren masana’antu da dama da sauran mahalarta taron da suka hada da wasu gwamnonin jihohi ne suka halarci taron wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shattima. Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shattima. REUTERS - Afolabi Sotunde

Taron dai an shirya shi ne domin tattauna ra'ayoyin da za a bi don farfado da masana'antar auduga da masaku a Najeriya. A jawabinsa na bude taron, mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima ya kalubalanci mahalarta taron da su samar da taswirar farfado da fannin auduga da masaku a Najeriya,da kuma  ba da tabbacin cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta yi kokarin ganin Najeriya ta yi amfani da damammaki a da take da su a fanin noman auduga don cimma wannan mataki a Afrika da ma duniya baki daya.

Mataimakin ShugabanNajeriya  Kashim Shettima Mataimakin ShugabanNajeriya Kashim Shettima via thisday

Yan lokuta da kamala taron,Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya ce taron zai baiwa Najeriya damar sake farfado da masana’antar masaku da ke cikin kasar domin samar da ayyukan yi,y ana mai matukar farin ciki da kasancewa cikin wannan tattaunawa da za ta sake kawo gyara ga tattalin arzikin kasar ga baki daya.

Shugaban majalisar kulada tattalin arziki ta Najeriya, Kashim Settima. Shugaban majalisar kulada tattalin arziki ta Najeriya, Kashim Settima. © Daily Trust

A daya wajen mataimakin Shugaban kasa,Kashim Shettima y ana mai kira ga daukacin yan kasar da su hada kawunansu,musaman arewacin kasar na ganin shugabanin al’uma sun yi amfani da damar da suke da ita wajen hada kawunan jama’a da kuma yafewa juna da nufin ci gaban jama’a ga baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)