Gwamnatin Najeriya ta yi iƙirarin biyan naira tiriliyan 7 na tallafin man fetur

Gwamnatin Najeriya ta yi iƙirarin biyan naira tiriliyan 7 na tallafin man fetur

A cewar Gwamnatin namijin ƙoƙarin da ta yi wajen zuba wannan maƙuden kuɗaɗe su ne suka taimaka wajen hana hauhawar farashin man na fetur ta yadda har ta kai ana iya sayen man da sauƙi a yanzu.

Sanarwar da gwamnatin Najeriyar ta fitar ta ce ta sanya wannan tallafi ne daga watan Agustan bara zuwa Disambar shekarar nan.

Duk da wannan iƙirari na gwamnati, har yanzu wasu sassan ƙasar musamman a yankin arewaci na sayen man a farashin kusan naira dubu guda kan duk lita guda.

Tuni ƙungiyoyin fararen hula suka fara sukar wannan iƙirari na gwamnati wanda ke zuwa bayan fitar wasu rahotanni daga kafafen yaɗa labaran ƙasar da ke cewa har yanzu Najeriyar na biyan tallafin man fetur a ɓoye.

Wannan sanarwar ta gwamnati na zuwa ne a dai dai lokacin da al'ummar Najeriyar suka faɗa wata sabuwar matsalar ƙarancin man fetur wanda ya haddasa dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai.

Tun farko wani rahoto da jaridar The Cable a Najeryar ta wallafa ne ya bayyana cewar shugaban ƙasar Bola Tinubu ya amince ayi amfani da ribar shekarar 2023 da kamfanin mai na ƙasar NNPCL ya tattara wajen biyan tallafin man fetur.

Rahoton ya ce shugaban ya amince da haka saboda damuwar da kamfanin ya nuna bisa ƙarancin shige da fice na kuɗaɗe tun bayan cire tallafin man fetur a ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)