Gwamnatin Najeriya ta tattaunawa da China don samar mata wurin ƙera makamai

Gwamnatin Najeriya ta tattaunawa da China don samar mata wurin ƙera makamai

Ministan harkokin waje na Najeriya Ambasada Yusuf Tuggar ne ya tabbatar da haka a lokacin da yake karɓar baƙuncin ministan harkokin wajen China Wang Yi a birnin tarayyar ƙasar Abuja.

A tattaunawarsa da RFI Hausa jim kadan bayan kammala ganawar Tuggar ya ce sun sake duba yarjejeniyoyin da aka ƙulla tsakanin China da Najeriya a baya tare da jaddadasu da kuma bibiyar batutuwan.

A fannin tsaro ministan ya ce suna aiki tare da kuma kyautata alaƙar aiki wurin horar da jami’an soji da sauran ma’aikatan sojin ƙasar cikin har da samar da wurin ƙera makamai a Najeriya ta yadda ƙasar za ta daina fuskantar ƙalubale wurin ƙin sayar mata makamai daga ƙasashen ƙetare

A fannin tattalin arziƙi ministan tsaro Ambasada Tuggar ya ce tuni aikin layin dogo daga Kano zuwa Maraɗi ta Jamhuriyar Nijar da kuma Kano zuwa Jigawa ya kai kashi kusan 40 wanda a wannan ɓangaren ma China za ta zuba kuɗi domin tabbatar da ci gaban aiki.

Ministan wajen na Najeriya Yusuf Tuggar ya ce ziyarar ministan harkokin wajen na China na nuna irin yadda suka bai wa Najeriya muhimmanci a nahiyar Afrika.

Ministan Harkokin Wajen Najeriya Ambasada Yusuf Tuggar 03:50

Domin nuna wannan labarin, akwai bukatar ka bayar da izinin sanin bayanan masu bibiya da tallace-tallacen kundin adana bayanai na cookies

Amince Zabin son raina Ministan Harkokin Wajen Najeriya Ambasada Yusuf Tuggar © RFI Hausa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)