Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da aniyar ƙarin harajin VAT a ƙasar

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da aniyar ƙarin harajin VAT a ƙasar

Ministan kudin kasar Wale Edun ne ya bayyana hakan yayin taron masu zuba hannun jari da IMF bankin duniya na shekara shekara da ya gudana a birnin Washington.

Ministan ya ce kudirin ƙarin kudin harajin yana gaban majalisar dokokin ƙasar, wanda zai shafi akasari kayayyakin alatu, za a aiwatar da shi ne daƙi-daƙi.

Edun ya ce kayayyaki masu mahimmanci da talakwa ke amfani da su za su ci gaba da kasancewa babu harajin VAT, ko kuma ma babu harajin gaba ɗaya, inda ya ƙara da cewa nan ba da jjimawa ba za a fito da jerin kayayyakin da ba za a ɗora musu haraji ba.

A watan Satumba, shugaban kwamitin da shugaban ƙasar ya don sake fasalin haraji,  Taiwo Oyedele ya ce kwamitin yana tayin wani ƙudirin doka da zai tanadi ƙarin harajin VAT ga majalisar dokokin ƙasar, don neman ƙarin VAT ɗin daga kashi 7.5 zuwa kashi 10.

Gwamnatin Najeriya a ƙarƙashin shugaba Bola Tinubu tana ɗaukar wannan mataki ne duk da matsanancin halin matsin rayuwa da talakawan ƙasar ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)