Gwamnatin Najeriya ta rushe ma'aikatar wasanni

Gwamnatin Najeriya ta rushe ma'aikatar wasanni

Bayanin rushe ma’aikatun na zuwa ne ta cikin wani dogon jawabi da mai magana da yawunsa Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na Twitter yau Laraba, jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartaswa.

Sanarwar ta ce a yanzu za’a samar da sabuwar ma’aikata wadda zata kula da dukannin yankunan ƙasar a maimakon yankin Neja Delta kadai.

Sanarwar ta  kuma kara da cewa a yanzu harkokin wasanni na ƙasar baki daya zasu koma ƙarƙashin hukumar kula da wasanni ta ƙasa.

Baya ga wannan kuma shugaban ya haɗe ma’aikatar yawon bude idanu  da ma’aikatar al’adu da tattalin arziki na zamani zuwa ma’aikata guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)