Gwamnatin Najeriya ta kwace kwangilar hanyar Abuja-Kaduna daga hannun kamfanin Julius Berger

Gwamnatin Najeriya ta kwace kwangilar hanyar Abuja-Kaduna daga hannun kamfanin Julius Berger

Bayan cikar wa’adin kwanaki 14 da gwamnatin ta baiwa kamfanin na ɗaukar mataki kan tafiyar wahainiya da aikin ke yi, a yanzu ta sanar da ficewa daga yarjejeniyar ba tare da samun damar yin wata tattaunawa ba.

Baya ga  tafiyar wahainiya da aikin ke yi, ana kuma zargin sa da ƙin bada cikakken bayani kan kuɗin da aikin ya laƙume kawo yanzu, ƙin biyayya ga dokokin da aka shimfida, da kuma ƙin biyayya ga shawarwarin da ma’aikatar ayyuka ta bashi.

An dai shafe tsahon watanni ana yamutsa gashin baki tsakanin kamfani da gwamnati kan waɗannan matsaloli da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa.

Ta cikin sanarwar da ma’aikatar ayyukan ta fitar mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaranta Mohammed Ahmed ta ce an shafe watanni 13 a jere ana tattaunawa da kamfanin amma an kasa cimma matsaya, don haka babu wani zabi da ya wuce kawo ƙarshen yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)