Gwamnatin Najeriya ta janye tuhuma kan yaran Kano masu zanga-zangar yunwa

Gwamnatin Najeriya ta janye tuhuma kan yaran Kano masu zanga-zangar yunwa

Kafin yanzu dai kotun ta gindaya sharuɗɗan biyan Naira miliyan 10 kan kowanne yaro guda baya ga buƙatar tsayawar babban jami’in gwamnati da ya kai mataki aiki na 15, gabanin bayar da belin yaran yayinda kuma kotun ta ɗage shari’ar zuwa watan Janairun baɗi.

Tun bayan faduwar yara 4 cikin waɗanda ake tuhuma a gaban kotun yayin yi musu shari’a ranar Juma’ar da ta gabata, ministan shari’ar Najeriyar Lateef Fagbemi ya umarci dawo da takardun shari’ar yaran zuwa ofishinsa.

Wasu daga cikin yaran da mahukuntan Najeriya suka tsare tsawon kwanaki 93. Wasu daga cikin yaran da mahukuntan Najeriya suka tsare tsawon kwanaki 93. © dailytrust

Sai dai bayan juyewar batun zuwa kace-nace a wasu sassa na ƙasar baya ga shiga tsakanin ƙungiyoyin fararen hula da na kare haƙƙin dan adam, kotun a safiyar yau Talata ta sanar da sallamar shari’ar yaran.

A wani labari na daban da kakakin gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana cewa kowanne lokaci a yau Talata ne ake sa ran Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi yaran a gidan gwamnatin jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)