Gwamnatin Najeriya ta fara sayar wa matatar Ɗangote ɗanyen mai a farashin naira

Gwamnatin Najeriya ta fara sayar wa matatar Ɗangote ɗanyen mai a farashin naira

Sanarwar ta ce biyo bayan taron da aka yi don tsara aiwatar da wannan shiri a karkashin jagorancin ministan kudin ƙasar, Wale Edun, an fara sayar da mai a kan farashin naira a hukumanci.

A ranar 29 ga watan Yuli majalisar zartarwar Najeriya ta amince da umurnin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar na a fara sayar wa da matatar man Ɗangote da sauran matatun mai na ƙasar ɗanyen mai a farashin naira.

Kwanaki bayan haka ne, gwamnatin ta sanar a hukumance cewa za ta riƙa sayar wa da matatun mai ɗayen maia a farashin naira daga ranar 1 ga watan Oktoba.

Idan ba a manta ba kamfanin mai na Najeriya da rukunin kamfanonin Ɗangote su ka shiga takun-saƙa a kan batun ɗanyen mai, amma daga bisani aka sasanta su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)