Gwamnatin Najeriya ta fara jigilar fasinjoji kyauta a jirgin ƙasa

Gwamnatin Najeriya ta fara jigilar fasinjoji kyauta a jirgin ƙasa

Muƙaddashin daraktan hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya Ben Iloanusi ne ya sanar da haka yayin da ya karɓi rukunin farko na fasinjojin da za su ci gajiyar tafiya kyauta.

Fasinjojin runkunin farko sun tashi ne daga tashar jirgin ƙasa ta Kubuwa dake Abuja zuwa Rigasa ta jihar Kaduna.

Ben ya ce hukumar na ɗaukar matakan da ya kamata domin tabbatar da tsaron fasinjoji yayin da suke kan hanyar zuwa garuruwansu a jiragen ƙasan Najeriya.

Ya ci gaba da cewa kimanin mutum dubu 20 ne za su amfana a jigilar fasinjojin kyauta ta jirgin ƙasa a kowaccce rana, kuma ana sa ran mutum dubu 340 cikin mako guda da za a kwashe ana ɗaukar fasinjojin kyauta.

Hukumar kula da jiragen ƙasar ta Najeriya ta ce ɗaukar fasinjojin kyauta za a yi shi tsakanin Abuja zuwa Kaduna da Lagos zuwa Ibadan da Warri zuwa Itakpe da Fatakwal da Aba.

Da yake tsokaci kan yuwuwar yin muna-muna a ɗaukar fasinjojin kyauta muƙaddashin daractan hukumar jirage ƙasa ta Najeriya Ben Iloanusi ya ce sun buɗe shafin yanar gizo domin bai wa kowa dama da kuma zai taimaka wurin tabbatar da ba a sayarwa da mutane tikiti ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)