Gwamnatin Najeriya ta dakatar da kamfanin jirgin saman Max Air daga aiki

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da kamfanin jirgin saman Max Air daga aiki

Hukumar kula da sufurin jiragen saman ƙasar ce ta sanar da dakatarwar na tsawon watanni 3, kamar yadda sanarwar da daraktan yaɗa labarai da kula da walwalar jama'a, Michael Achimugu ya fitar ta bayyana.

Jirgin Max Air ya fuskanci birgewar taya yayin saukarsa a filin jirgin saman Malam Aminu Kano wanda ya taso daga jihar Legas, a wani yanayi da hakan ke zama karo na 3 da jirgin ke samun matsala cikin watanni 3.

Ko da yake fasinjoji da jirgin ke ɗauke da su kimanin 53 basu samu ko rauni ba, amma an rufe ayyukan tashin jirage a filin jirgin saman har sai da hukumar kula da filayen jiragen sama ta sanar da buɗewa a safiyar yau Laraba.

A halin yanzu ana jiran hukumar binciken hatsura ta ƙasar ta gudanar da bincike don gano musabbabin faruwar lamarin, yayin da dakatarwa Max Air za ta fara aiki ranar 31 ga watan Janairu, domin basu damar gyara yanayin ayyukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)