Ministan Kuɗi Wale Edun ya bayyana haka tare da alkawarin ci gaba da tallafa wa mutane miliyan guda a kowanne wata.
Edun ya ce shirin zai ci gaba da tafiya har zuwa lokacin da za su rika bai wa mutane miliyan guda tallafi kowanne mako ko makonni bibbiyu.
Ministan ya kuma ƙara da cewar gwamnati na ɗaukar kwararan matakai wajen ganin ta inganta harkar noma da samar da abinci domin ganin an rage dogara ga ƙasashen ketare wajen shigar da abincin kasar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan ƙasar ke ci gaba da kokawa kan tsadar rayuwa, al'amarin da ya tilasta musu gudanar da zanga-zanga domin nuna ɓacin ransu kan raɗaɗin da suke fama da shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI