Gwamnatin Najeriya ta ce an samu sassaucin garkuwa da mutane a kasar

Gwamnatin Najeriya ta ce an samu sassaucin garkuwa da mutane a kasar

 

Shugaban cibiyar yaƙi da ta’addancin ta Nijeriya, Manjo Janar Adamu Laka ne ya bayyana sabon rahoton ga manema labarai ranar Alhamis a Abuja.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa duk da sauƙin da aka samu, har yanzu matsalar satar mutanen na cigaba da zama babbar barazana ga tsaron ƙasa, ta fuskar gurgunta tattalin arziƙi musamman ayyukan noma a yankunan karkara.

Janar Adamu, ya ce ta’addancin satar mutanen a Nijeriya ta ragu ne da kashi 16.3 cikin 2024, idan aka kwatanta da yadda lamarin yayi ƙamari a shekarar 2023.

Daga cikin kaso 61.1 da aka samu na yin garkwa da mutane domin karbar kuɗin fansa a faɗin ƙasar kuwa, jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara ne ke kan gaba da kaso 13.8 na adadin laifukan ta’addancin da aka aikata da kuma yawan mutanen da aka sace.

Daga ƙarshe, rahoton yayi hasashen za a ci gaba da fuskantar matsalar satar mutane dan kuɗin fansa cikin wannan shekara, saboda maƙudan kuɗaɗen da miyagu ke samu daga ta’addancin, sai dai tuni gwamnati ta tsaurara matakan yaƙi da matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)