Gwamnatin Najeriya ta ɗage haramcin haƙar ma'adinai a jihar Zamfara

Gwamnatin Najeriya ta ɗage haramcin haƙar ma'adinai a jihar Zamfara

Da yake bayyana hakan ta cikin sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai Segun Tomori ya fitar yau Lahadi, ministan kula da albarkatun ƙarƙashin ƙasa na Najeriya, Dele Alake ya ce bayan duba kan halin da tsaron jihar ke ciki a halin yanzu, shugaban ƙasar da mai taimaka masa kan tsaro, sun sahale a dawo da haƙar ma’adinai a Zamfara.

Alake ya ce matakin zai bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar kasancewar Zamfara na da tarin albarkatun ƙarƙashin ƙasa, kamar su zinare da ma’adinin lithium.

Alake ya ƙara da cewa matakin dakatar da haƙar ma’adinan a jihar ya tsayar da ayyukan albarkatun ƙasa cak a yankin, wanda wasu ke amfani da damar wajen haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Idan za’a iya tunawa a shekarar 2019 ne tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya sanya haramcin haƙar ma’adinai a Zamfara, baya ga ayyana jihar a matsayin wadda aka haramta shawagin jiragen sama a shekarar 2021, saboda ta’azzarar matsalar rashin tsaro a yankin.

Matsalar rashin tsaro na hare-haren ƴan bindiga da jihar ta Arewacin Najeriya ke fuskanta dai na janyo asarar rayuka, baya ga tarin dukiyoyin jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)