Gwamnatin Najeriya na duba wasu hanyoyin samar da lantarki ga arewacin ƙasar

Gwamnatin Najeriya na duba wasu hanyoyin samar da lantarki ga arewacin ƙasar

Ministan wutar lantarki na Najeriya Adebayo Adelabu wanda ya bayyana haka, ya ce gwamnatin tarayya ta fara ɗaukar matakai na laluɓo wasu hanyoyin samar da lantarki ga jihohi da ke arewacin Najeriya.

Ministan ya ce gwamnatin za ta ɗauki matakin ne domin rage raɗaɗin rashin wutar da yankin arewacin Najeriya ke fama da shi sakamakon lalatacewar layukan samar da hasken wuta a faɗin yankin.

Mista Adebayo ya bayanna hakan ne bayan wata ganawa da ya yi da shugaban ƙasa Bola Tinubu a wannan Litinin, inda ya ce za’a fara amfani da wata kwarya-kwaryar tashar bayar da lantarki ta Ikot Ekpene wadda ta fito daga Calabar domin kai lantarki yankin arewa, sai dai layin ya lalace.

Ya ce sun gano abin da ya janyo matsalar, wanda ya samo asali sakamakon lalata layukan samar da wuta na cibiyar Shiroro

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)