Gwamnatin Najeria ta musanta tilastawa Buhari gurfana a gaban kotu

Gwamnatin Najeria ta musanta tilastawa Buhari gurfana a gaban kotu

Rahotanni daga kafofin da dama sun ce gwamnatin Bola Tinubu ta tilastawa tsohon shugaban kasar amsa tambayoyi a gaban masu shiga tsakanin dangane da kwangilar dala biliyan 6 ta gina tashar da aka soke.

Mai magana da yawun shugaba Tinubu, Bayo Onanuga ya musanta zargin da kuma watsi da shi a matsayin cewar babu wani mai kama da haka.

Onanuga ya bayyana labarin a matsayin na kanzon kurege inda yake cewa babu gaskiya gwamnatin ta aikata haka.

Mai magana da yawun shugaban ya ce akwai wani zama makamancin haka da aka yi wanda bai dace ace an ruwaito shi a kafofin yada labarai ba, har sai masu shiga tsakanin sun amince da hakan.

Onanuga ya ce yayin da suke mutunta shiga tsakanin, yana da muhimmanci jama'a su san cewar shugaba Tinubu bai tilastawa wani gabatar da ba'asi a kan lamarin ba.

A karshe, Kakakin gwamnatin ya ce shugaban ya yabawa daukacin fitattun mutanen da suka bada ba'asi kan lamarin.

Rahotanni sun ce soke kwangilar gina tashar Mambilla ya sa kamfanin da aka bai wa aikin gabatar da kara a Paris, abinda ya sa aka bukaci wasu jiga jigan gwamnatin da ta gabata gurfana domin bada ba'asi a kan lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)