Gwamnatin Katsina ta jaddada matsayarta na ƙin rungumar sulhu da ƴan ta'adda

Gwamnatin Katsina ta jaddada matsayarta na ƙin rungumar sulhu da ƴan ta'adda

Gwamnan jihar Malam Dikko Rada ya bayyana haka lokacin da ya karɓi kwamandan runduna ta 8 ta sojin Najeriya dake Sokoto, kuma kwamandan yaki da ƴan ta'adda Manjo Janar Ibikunle Ademola Ajose.

Radda ya ce gwamnatinsa za ta karbi shirin zaman lafiya da 'yan ta'adda ne kawai akan wasu sharidodin da zasu tabbatar da zaman lafiya mai dorewa, kuma idan bukatar hakan ta taso ne za'a yi ta ne da goyan bayan jama'ar dake yankunan da ake fama da matsalar.

Gwamnan ya ce an kafa kwamitin tintiba wanda ya kunshi masu ruwa da tsaki daga yankunan da ake fama da matsalar tsaron domin tabbatar da zaman lafiya da kuma taimakawa tubabun 'yan bindigan da suka aje makamansu aka kuma rungume su a cikin al'umma.

Radda ya kara da cewar wadannan ƴan bindigar ƴan uwansu ne da aka haifa a tsakanin su amma suka zabi daukar makami domin yiwa jama'a illa, saboda hak awadanda suka tuba za su samu taimakon daga gwamnatinsa.

Gwamnan ya ce a shirye suke su tallafa da kudade da kuma dabbobi domin sake tsugunar da wadanda suka yi wasti da wannan mummunar dabi'ar.

Daga karshen gwamnan ya jinjinawa jami'an rundunar soji da ƴan sanda da ƴan sakai saboda rawar da suka taka wajen samar da tsaron da ya kai ga jama'a zuwa gonakinsu suyi aiki a daminar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)