Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa gwamna kan yaɗa labarai, Sunusi Bature ya fitar a wannan Alhamis.
A cikin sanarwar, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce, wannan tallafin gidajen zai taimaka matuka wajen rage raɗaɗin tasiri da ambaliyar ruwan ta haddasa tare da bai wa magidanta damar tsugunar da iyalansu wuri guda.
Gwamnan Abba ya ce, gwamnatinsa na aikin haɗin guiwa da Ma'aikatar Jin-ƙai da Rage Raɗaɗin Talauci domin samar da abinci da wasu kayayyaki ga mutanen da lamarin ya shafa.
Mutane da dama ne a sassan Najeriya suka gamu da ibtila'in ambaliyar ruwa a bana a ƙasar, lamarin da ya raba dubbai da muhallansu.
Ambaliyar ruwan da aka gani a baya-bayan nan a birnin Maiduguri da ke jihar Borno ta shafi akalla mutane miliyan 2 kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar.
A ɓangare guda, masana yanayi sun yi hasashen cewa, nan da wasu ƴan makwanni za a samu jerin ambaliyar ruwa a wasu jihohin Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI