Gwamnatin Kano ta bayar da tallafin N100m ga wadanda ambaliyar Borno ta shafa

Gwamnatin Kano ta bayar da tallafin N100m ga wadanda ambaliyar Borno ta shafa

Tawagar gwamnatin jihar Kano, ƙarkashin jagorancin wakilan Gwamna Abba Yusuf da suka haɗa da Kwamishiniyar Agajin Gaggawa da yakar Talauci, Hajiya Amina Sani da takwaranta na Yada Labarai Baba Dantiye ne suka mika wa Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum cakin kudin tallafin.

A ziyarar da su kai fadar gwamnanti a Maiduguri, Dantiye ya bayyana daɗɗiyar ƴan uwantaka da zumuncin dake tsakanin jihohin Kano da Borno.

Da ya ke mika sakon jajen gwamnatin Kano a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya jajanta wa wadanda abin ya shafa, inda ya bayyana lamarin a matsayin wani babban bala’i na jin kai da aka ɗaɗe ba'a ga irinsa ba, tare da yin kira da a tallafa wa mutanen da abin ya shafa.

Tawagar gwamnatin jihar Kano a fadar gwamnatin Borno da ke Maiduguri.15/09/24 Tawagar gwamnatin jihar Kano a fadar gwamnatin Borno da ke Maiduguri.15/09/24 © RFI Hausa / Ahmed Abba

Wakilin gwamnan ya ce  gwamnan Kabir na jaddada goyon bayansa ga al'ummar Maiduguri tare da tallafa musu a kowane lokaci, inda ya ce irin wadannan masifu na bukatar taimakon hadin gwiwa.

Ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu a ambaliyar, ya kuma yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata da rasa dukiyoyinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)