Shugaban karamar hukumar Honarabul Gbenga Olaleye Akinola a madadin Gwamnatin Jihar shi ne ya mika kayan tallafin a ranar Lahadi a lokacin da ya jagoranci tawagar jami'an Gwamnati zuwa kauyen Gbenpakan inda wasu mahara dauke da makamai suka yi wa Fulanin kisan gilla.
Daya daga cikin kasuwanin dabobi Laeticia Bezain/RFIDa yake karbar kayan a madadin iyalan mamatan, Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen Jihar Oyo Alhaji Ibrahim Jiji ya fara da nuna godiya ne ga Gwamna Seyi Makinde da Mataimakin sa Alhaji Bayo Lawal da Kwamishinan 'yan sandan Jihar CP Sonubi Ayodele a kan hanzarta daukar matakin ziyartar wannan kauye da suka yi bayan kwana 2 da aukuwar lamarin inda suka jajantawa iyalan mamatan da ba su hakuri tare da yi musu alkawarin bankado masu hannu wajen aikata wannan danyen aiki domin hukunta su.
bikin mika kayan abinci ga mutanen da rikicin ya ritsa da su © rfi hausaA wannan ziyarar ne Mukadashin Gwamnan Jihar Bayo Lawal ya mika wa iyalan mamatan kudi naira miliyan daya domin rage musu radadin iftila'in da ya rutsa da su.
Shugaban na Miyetti Allah wanda ya nuna damuwa da kalaman jagoran hukumar (NEMA) ya ce "irin wadannan kalamai alama ce ta rashin iya aiki wanda ya kamata mahukumta su hanzarta daukar matakin bin diddigi da yin binciken kwakwaf a kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI