Rundunar ‘yan sandan Finland ta ce an kama Simon Ekpa tare da wasu mutane hudu a ranar Alhamis bisa zargin ta’addanci. Rahotanni na nuni cewa Ekpa “ya bayar da gudunmawa wajen tashe-tashen hankula da cin zarafin jama’a a Kudu maso Gabashin Najeriya.”
Yankin Enugu, tsohon babban birnin yankin Biafra © Wikimedia Commons CC0 Martin KudrEkpa ya jagoranci Autopilot, wani bangare na masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB),wata kungiya da ke jagorantar fafutukar neman kafa kasar Biafra mai cin gashin kanta wacce take son a zartas da ita daga Kudu maso Gabas da wasu sassan Kudu-maso-Kuduncin Najeriya. Gwamnatin jihar Enugu ta yaba wa hukumomin kasar Finland bisa kame Simon Ekpa da ke da zama a kasar Finland, wata kasa ta Arewacin Turai.
Sakataren gwamnatin jihar Chidiebere Onyia ta ce gwamnatin jihar ta yi imanin cewa mai fafutukar kafa kasar Biafra “mai laifi ne na kowa, dan damfara, kuma dan ta’adda, wanda ba ya da ra’ayin ‘yan kabilar Igbo a zuciya.” “Gwamnatin ta kuma bayyana Ekpa a matsayin mai kisan kai kuma dan damfara, wanda yake jin dadin kashe al’ummarsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI