Taron na kwanaki biyu dai, an shirya shine don sauya fasalin tsarin karatun tsangaya, wanda aka gada iyaye da kakanni a yankin Arewacin ƙasar.
Da yake gabatar da jawabinsa, shugaban Hukumar Kulada Karatun Tsangaya da kuma Yaran da basa zuwa makaranta ta ƙasar Dr Muhammad Sani Idris, ya buƙaci gudunmuwar gwamnati wajen samar da cibiyoyin bada horon harsunan Larabci da Turanci da kuma dabarun haddace Al-Qur'ani mai tsarki.
Gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce ta hanyar samar da ilimi ga kowa ne za a samu damar magance matsalar masu tada kayar baya.
Ku latsa alamar sauto don jin rahoton wakilinmu na Maiduguri Bilyaminu Yusuf........
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI