Ma’aikatar yaɗa labarai da lura da harkokin cikin gida ta jihar ce ta fitar da sanarwar a shafinta na Facebook yau Talata. Ta buƙaci alumma da su ƙauracewa amfani da kayan miyan saboda gudun kamuwa da cutuka.
“saboda ambaliyar da aka samu kayan miyan da suka fito daga inda lamarin ya shafa sun gurbata da ƙwayoyin cuta da turoso da gawawwaki da sinadarai masu illa”
“Yin amfani da kayan miyan zai iya haddasa illa sosai ga lafiya wanda ya haɗar da cutukan dake yaduwa a ruwa da ƙwayar cuta da ake samu a abinci da sauran matsaloli na lafiya” a cewar sanarwar
Ma’aikatar ta yi kira ga jama’a da su tabbatar suna sayan kayan miya da ganyayyaki daga wuraren da suka gamsu da ingancinsu tare da wanke duk abinda suka saya kafin su yi amfani da shi
Ta kuma yi kira ga alumma su baiwa lafiyarsu muhimmanci tare da tsare kawunansu a wannan yanayi da ake ciki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI