Gwamnan Yobe ya karbi ragamar jagorancin kungiyar Tafkin Chadi

Gwamnan Yobe ya karbi ragamar jagorancin kungiyar Tafkin Chadi

Yayin jawabin karbar ragamar jagorancin kungiyar, Gwamna Buni ya yi alkawarin mayar da hankali wajen aiwatar da shawarwari da kuma yarjeniyoyin da taron ya amince da su tare da ci gaba da tintibar wakilan kungiyar domin ganin ci gaban jama'ar yankin.

Gwamnan ya ce yana fatar samun hadin kai mai tasiri da goyan baya daga wakilan kungiyar wajen ganin sun samu nasarar kudirin da suka sanya a gaba na tabbatar da tsaron yankin da kuma inganta rayuwar jama'ar su wadanda ke fuskantar kalubale daban daban.

Gwamnan Yobe Mai Mala Buni da takwararsa ta Chadi Ildjima Abdraman Gwamnan Yobe Mai Mala Buni da takwararsa ta Chadi Ildjima Abdraman © YBSG

Buni wanda ya godewa takwarorinsa saboda karrama shi da suka yi wajen ba shi jagorancinsu na shekaru 2 masu zuwa, yayin da ya ce zai yi aiki tare da su a koda yaushe domin tinkarar duk wata matsalar da ka iya tasowa da kuma aiwatar da yarjeniyoyin da suka amince da su.

Gwamnan ya ce a shirye yake ya kuma yi aiki tare da kawayen su irin su kungiyar kasashen Afirka da kasashen duniya da kuma majalisar dinkin duniya wajen samarwa yankin ci gaba.

Daga karshe Buni ya jinjinawa gwamnan Hadjer Lamis dake kasar Chadi, wato Ildjima Abdraman wadda ta mika masa ragamar jagorancin bayan kawo karshen wa'adin mulkin ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)