Gwamnan Kano ya yaba da yadda ake gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, jim kaɗan bayan kaɗa ƙuri’arsa a ƙaramar hukumar Gwale.

Gwamnan ya yi la’akari da cewar zaɓen da ke gudana a mazaɓu 484 na ƙananan hukumomi 44 da ake da su a jihar, shi ne mafi inganci a tarihin jihar.

Ya bada tabbacin cewa waɗanda aka zaɓa za su yi wa al’umma aikin da suke buƙata tare da tabbatar da gwamnati ta gari.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma buƙaci ƴan adawa da su amince da shan kaye, inda ya ce hakan kuwa zai faru ne sakamakon irin goyon bayan da jam’iyarsa ke da shi.

Ina so in yi kira ga ƴan adawa da su amince da shan kaye a kodayaushe, saboda muna da rinjaye wajen goyon bayan masu kada kuri'a.

Anta kai ruwa rana gabanin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin da ake yi a yau, sakamakon yadda aka samu hukunce-hukunce kotu masu cin karo da juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)