Gwamnan Kano Abba ya sauke sakataran gwamnati da kwamishinoni 5

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun daractan yaɗa labaran gwamnan na Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa ya tabbatar da matakin da gwamnan ya ɗauka yau Alhamis.

Kwamishinonin da gwamnan ya sauke daga muƙamansu sun haɗa da kwamishinan yaɗa labarai Baba Halilu Dantiye da kwamishina a ma’aikatar kuɗi Ibrahim Jibril Fagge da kwamishinar al’adu da yawon buɗe ido Ladidi Ibrahim Garko da kwamishinan ayyuka na musamman Shehu Aliyu Yammedi da kwamishinan  raya karkara Abbas Sani Abbas.

Baya ga haka gwamnan ya sauyawa mataimakinsa Aminu Abdulssalam ma’aikatar da yake lura da ita a matsayin kwamishina wato ta ƙananan hukumomi zuwa ma’aikatar ilmi mai zurfi.

Gwamanan na Kano Abba Kabir Yusuf ya kuma sauyawa kusan dukkanin kwamishinonin jihar ma’aikatun da za su lura da su.

Matakin na zuwa kwanaki kaɗan bayan bullar wata tafiya mai suna Abba Tsaya da Kafarka, da ke rajin ganin gwamnan ya raba gari da mai gidansa na siyasa kuma jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya Sanata Rabi’u Musa Kwanwaso

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)