A taron miƙawa ƴan takarar shugabancin ƙananan hukumomi na jamiyyar NNPP tuta, gwamnan ya sha alwashin cewar babu gudu ba ja da baya za su gudanar da zabe a Kano.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
A ranar Talata ne wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin mai shari’a Simon Ameboda ta rushe shugabanni da mambobin hukumar zaben jihar KANSIEC tare da dakatar da gudanar da zaben har sai an gyara tsarin shugabancin hukumar yadda ya kamata.
Gwamnan, ya ce a halin yanzu jihar ba za ta bari wasu suzo su dagula zaman lafiyar da ake samu ba, yana mai cewa gwamnatin jihar da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar KANSIEC na da dukkan goyon bayan da tsarin mulki ya ba shi wajen gudanar da zaben.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI