Gwamnan Filato ya ƙaryata zargin hana kiran salla da lasifika a masallatan jihar

Gwamnan Filato ya ƙaryata zargin hana kiran salla da lasifika a masallatan jihar

Muftwang ya zargi masu yaɗa wannan jita-jitar a matsayin waɗanda ba sa son zaman lafiya a jihar.

A kwanakin nan ne dai labari ya bazu a shafukan sada zumanta na cewa za'a haramta kiran sallaha a jihar Filato da ke Arewa maso tsakiyar Najeriya.

A halin yanzu gwamnan ya ce babu wani dalili da zai sanya shi hana kiran sallah da lasifika a masallatan jihar, domin a cewarsa doka ta bai wa kowa damar gudanar da addininsa cikin kwanciyar  hankali ba tare da samun tsaiko daga gwamnati ko ɗaiɗaikun jama'a ba.

Daga bisani Caleb ya yi kira da al'umma su riƙa ƙoƙari wajen tantancewa tsakanin labarin gaskiya da na ƙarya, saboda gujewa yada abinda ka iya haifar da tashin hankali tsakanin al'ummar jihar da na ƙasar baki ɗaya.

Latsa alamar sauti domin sauraren abinda gwamnan ke cewa...

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)