A sanarwar da mai magana da yawun hukumar Olusegun Ogungbemide ya fitar, ya ce tankar man ta samu matsalar birki da ya sanya ta kwacewa matuƙinta tare da faɗawa cikin gwamman motoci a kan wani babban titi.
Sanarwar ta ce mutane 10 sun tsira da rayukansu ɗauke mabanbantan raunuka, baya ga wasu 3 da suka tsira babu ko ƙwarzane, sai dai wasu 18 sun ƙone ƙurmus da bama a iya gane su.
Hatsarin tankar mai a Najeriya dai ya zama ruwan dare, a wani yanayi da mahukunta ke alaƙanta shi da rashin kyawun hanyoyi da kuma tuƙin ganganci da hakan ke janyo asarar rayuka da dama.
ko a ranar Asabar ɗin ƙarshen makon da ya gabata, sama da mutane 100 ne suka mutu sanadiyar fashewar wata tankar mai a garin Dikko da ke jihar Neja kusa da kan titin Abuja zuwa Kaduna, kuma wannan ne karo na 5 da irin haka ke faruwa cikin watanni huɗu a ƙasar, domin ko a cikin watan oktoban shekarar bara, kusan mutane 170 ne suka ƙone kurmus a jihar jigawa a irin hatsarin nan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI