Gobara ta kashe miji da matarsa a Kano

Gobara ta kashe miji da matarsa a Kano

 

Lamarin dai ya faru ne a ranar Juma’a a unguwar Rangaza (Inken) Layin AU da ke ƙaramar hukumar Ungogo a jihar.

A cewar mai magana da yawun Hukumar kashe gobara ta Kano, Saminu Yusif Abdullahi, hukumar ta samu kiran agajin gaggawa da misalin ƙarfe 01:45 na tsakar dare daga ɗaya daga cikin ma’aikatan ta, FS Ahmad Abubakar ya sanar da faruwar gobarar.

Ya ce, “Ma’aikatan da ke bakin aiki daga ofishin kashe gobara na Bompai sun halarci zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka isa wurin da misalin ƙarfe 01:51 na tskar daren, da isar su sai suka ga an samu nasarar shawo kan gobarar.

“Wurin da gobarar ta tashi a wani ginin bene ne, amma gobarar ta tashi ne a ginin ƙasa wanda ake amfani da shi a matsayin gidan zama, mai ɗakuna biyu inda wutar ta cinye.

“A halin da ake ciki, Muhammad Uba da matarsa ​​Fatima Muhammad, hayaƙin ne ya hana su fita, an kuɓutar da su a sume da raunin ƙuna a wasu sassan jikinsu, daga baya kuma aka tabbatar da mutuwarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)