Wannan ya biyo bayan wasu rahotanni da suka karaɗe shafukan sada zumunta dake cewar Ganduje na yin wani sabon shiri domin sake tsige sarki Sunusi.
Idan ba’a mantaba an tsige sarkin Kano Muhammadu Sunusi II a zamanin mulkin tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje wanda a yanzu shine shugaban jamiyyar APC na Najeriya.
A wata sanarwa da ya fitar a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya yau Alhamis ta hannun Chief Oliver Okpala babban mai taimaka masa a fannin wayar da kan jama’a Ganduje ya nesanta kansa batun da ake yaɗawa cewar yana shiyra yadda za’a sake tsige sarkin Kano na 16 Muhammadu Sunusi II.
Sanarwar ta ce Ganduje bashi da wata alaka da batun naɗawa ko tsige Muhammadu Sunusi II. Ya ce yakamata jama’a su sani cewar a yanzu ba shine gwamnan Kano ko kakakin majalisar dokoki ba, don haka babu abinda ya shafeshi da sha’anin sarautar Kano.
Sanarwar ta ci gaba da cewa abin dariya ne Ganduje wanda ya bar mulkin Kano sama da shekara guda da ta wuce amma ana zarginshi da kitsa yadda za’a tsige ko naɗa sarki domin shi yanzu hankalinsa yana kan shugabancin da yake na jamiyyar APC da kuma bata gudunmawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI