Janye kudirin ya biyo bayan suka daga bangarori da dama, musamman fusatattun matasan dake jin radadin kuncin rayuwa. Shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas da kan sa ya gabatar da kudirin, wanda ya kai ga karatu na biyu kafin janye shi.
Dokar kuma ta bukaci daurin duk wani wanda aka samu da laifin lalata wani abu mai dauke da alamun kasa ko kuma wurin ibada ko kuma tinzira jama'a yin tashin hankali.
Kudirin yace duk wani wanda ya tare hanyar jama'a ko ya karkata hanyar jama'a ba tare da izini ba ko kuma hana jama'a fita daga gidajen su ba bisa ka'ida ko kuwa shirya zanga zanga ba tare da izini ba, zai biya tarar naira miliyan 2 ko daurin shekaru 5, ko kuma duka. Mai magana da yawun shugaban majalisar Musa Abdullahi Karshi ya sanar da janye kudirin dokar saboda fushin jama'ar kasa.
'Yan Najeriya da dama na nuna fushin su ga gwamnati dangane da abinda suka kira tsadar rayuwar da ta haifar da zanga zanga a makonnin da suka gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI