Umarnin na kunshe cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kula da gidajen yari na Najeriya reshen jihar Kano Musbahu Kofar Nasarawa ya fitar a jiya Litinin, inda ya ce an tantance nau’in fursunonin da suka samu ƴancin na shaƙar iska ƙarƙashin umarnin alƙalin alƙalan.
A cewar Musbahu Kofar-Nasarawa, galibin fursunonin an sallame su daga gidajen yarin ne sakamakon ko dai yanayi na lafiyarsu ko kuma waɗanda suka jima a tsare ba tare da yi musu shari’a ba.
Sanarwar ta ruwaito Alƙalin Alƙalan jihar ta Kano da ke arewacin Najeriya na bayyana cewa sakin fursunonin daga gidajen gyaran hali na matsayin makami da kan hana da dama aikata laifuka.
Rahotanni sun ce mai shari’a Dije Aboki ta kuma damƙa Naira dubu 10 ga kowanne Fursuna da aka fitar daga gidan gyaran halin.
Shugaban hukumar kula da gidajen yarin jihar Kano Mr Ado Inuwa ya yaba da matakin mai shari’ar wanda ya bayyana a kyakkyawan aiki da zai taimaka wajen rage laifuka a jihar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI