Fursunoni 3 sun lashe gasar Al-Ƙur’ani a Kano

Fursunoni 3 sun lashe gasar Al-Ƙur’ani a Kano

Fursunonin sun lashe gasar da Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Jihar Kano ta shirya a matsayin wani ɓangare na tsarin ilimin fursunoni.

An shirya musabakar ce da nufin sauya tunanin fursunoni domin su zamo mutane da al’umma za ta amfana da su bayan sun kammala zaman gidan yari.

Mai magana da yawun Hukumar Gidajen Yari a Jihar Kano, CSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya ce an shirya musabakar ce domin kyautata halayyar masu zaman gidan yari.

Ya bayyana cewa fursunan da ya lashe gasar yana tsare ne a gidan yarin Kumawa, inda ya samu kyautar Naira dubu dari.

Na biyu kuma a Gidan Yarin Goron Dutse yake tsare, kuma shi ma ya samu kyautar Naira dubu 50. Mutum na uku yana tsare ne a Gidan Yarin da ke Janguza kuma ya samu kyautar Naira dubu ashirirn.

Da yake jawabi a wurin taron, Shugaban Kungiyar Alarammomi, Gwani Shuaibu Shehu, ya yaba wa Kwamturolan Hukumar Gidajen Yari na Jihar Kano kan zurfin tunaninsa wajen shirya musabakar.

Ya kuma yaba masa da sama wa tsararrun wuraren da suka dace domin gudanar da al’amuran addini da sauran abubuwan da za su inganta rayuwarsu.

Gwani Shuaibu ya kuam yaba wa Ko’odinentan hukumar kan harkokin addinin, DSC Murtala Nasidi Kabara bisa yadda suke koyar da fursunonin karatun Al-Kur’ani..

A nasa jawabin, Kwanturolan hukumar, Ado Inuwa ya bayayan godiyarsa ga Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II bisa halartar gasar musabakar da kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)