Faruk Lawan ya tsinci kansa a Gidan Yarin Kuje ne bayan da kotu ta same shi da laifin nema da kuma karbar cin hancin Dala 500,000.
A watan Janairun 2024 ne Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin da aka yanke masa na zaman shekara biyar a gidan yari kan laifin karbar na-goron.
An kama Faruk Lawan da laifin neman cin hancin Dala miliyan uku daga attajiri Femi Otedola, a shekarar 2012, lokacin da tsohon dan majalisar ke jagorantar kwamitin binciken bakalar tallafin man fetur.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI